Shugabannin Faransa, Jamus, da Biritaniya: Sun kuduri aniyar farfado da tattaunawa da Iran
Kasashen Faransa da Jamus da Birtaniya sun bayyana aniyarsu ta farfado da shawarwari da Iran da Amurka dangane da shirin makamashin nukiliyar Iran da nufin cimma cikakkiyar yarjejeniya mai dorewa.
A cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa, kasashen uku sun yi la’akari da Shirin kunna yarjejeniyar fahimtar juna. A baya dai Faransa da Birtaniya da Jamus sun sanar da cewa za su ci gaba da neman hanyar diflomasiyya don warware rikicin, amma Iran ta tabbatar da cewa ba ta son ci gaba da tattaunawa a halin yanzu idan dai har za a kakaba mata takunkumi.
A gefe guda kuma shugabannin kasashen Birtaniya da Faransa da Jamus sun yi maraba da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a zirin Gaza tare da yin alkawarin dawo da taimakon jin kai da zarar an amince da yarjejeniyar.
A cikin sanarwar da suka fitar, shugabannin sun jaddada cewa, sun amince da cewa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya ba da cikakken goyon baya ga shirin na Gaza, da saukaka aiwatar da shi, tare da sa ido kan matakai na gaba.