Faransa Da Britaniya Da Jamus Sun Bukaci Iran Da Kada Ta Kai Wa Isra’ila Hari

Kasashen Faransa da Britaniya da Jamus sun yi kira ga Iran da kada ta kai wa Isra’ila hari, lamarin da kasashen uku suka ce zai

Kasashen Faransa da Britaniya da Jamus sun yi kira ga Iran da kada ta kai wa Isra’ila hari, lamarin da kasashen uku suka ce zai kara tayar da jijiyoyin wuya da kuma lalata duk wani shiri na yiwuwar tsagaita bude wuta.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, kasashen Ingila da Faransa da Jamus a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da gwamnatin Birtaniya ta fitar a yau litinin, yayin da suke neman Iran da kada ta kai wa Isra’ila hari, sun bukaci a kawo karshen yakin tare da sakin dukkan fursunonin da ake tsare da.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, al’ummar Gaza na bukatar agajin gaggawa.

Yanzu haka dai Isra’ila da kawayenta sun shiga cikin zullumi, sakamakon alwashin ramuwar gayya da Iran ta ce za ta mayar kan kisan shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas, Shahid Ismael Haniyeh a cikin kasarta.

Ita ma kungiyar Hezbollah da Hamas din duk sun sha alwashin mayar da martini kan kisan jiga-jigan nasu da Isra’ila ta yi.

Zaman dar-dar din da ake ci gaba da fuskanta a Gabas ta Tsakiya, ya dai sanya wasu kamfanonin jiragen sama tsawaita wa’adin dakatar da zirga-zirgar jiragensu a yawancin kasashen yankin.

Kamfanin jirgin sama na Air France ya soke zirga-zirgar jiragensa zuwa Beirut har zuwa nan da ranar Alhamis mai zuwa.

Shi ma na Lufthansa da Australia da kuma na Switzerland, sun ce jiragensu ba za su rika zuwa Tel Aviv da Tehran da kuma Amman ba har sai ranar 21 ga watan Augusta.

Sannan ya ce zai daina bi ta sararin samaniyar Iran da kuma Iraki har zuwa wannan lokaci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments