Falasdinu: Tsoro Ya Cika Zukatan Yahudawan A Yankin Yamma Da Kogin Jordan

Kafafen yada labarai na HKI sun bada sanarwan cewa gwamnatin HKI ta tsawaita aikin sojen da ta ke yi a yankin yamma da kogin Jordan

Kafafen yada labarai na HKI sun bada sanarwan cewa gwamnatin HKI ta tsawaita aikin sojen da ta ke yi a yankin yamma da kogin Jordan musamman a birnin Jenin bayan da ta gamu da turjiya mai tsanani daga dakarun falasdinawa masu gwagwarmaya a yankin.

Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa a jiya Talata ce yakamata sojojin yahudawan su kawo aikin aikin soje na musamman da suka fara a yankin yamma da kogin Jordan.

Labarin ya kara da cewa, yau kwanaki 8 kenan da fara aikin soje na musamman a wasu garuruwa a arewacin yankin yamma da kogin Jordan sai dai sojojin yahudawan sun kasa samun iko da wasu yankuna wadanda mayaka falasdinawa a Jenin suke iko da shi.

Wasu majiyoyin sun kara da cewa gwamnatin Natanyahu, a dole ta janye wasu sojojinta daga Gaza zuwa yankin yamma da kogin Jordan don murkushe falasdinawa a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments