Search
Close this search box.

Falasdinawa Bakwai Sun Shahada A Sansanin Jabaliya Sakamakon Hare-Haren Sojojin Isra’ila

Falasdinawa 7 ne suka yi shahada a wani mummunan hari da sojojin mamayar yahudawan sahayoniyya suka kai kan sansanin Jabaliya Falasdinawa bakwai daga iyali daya

Falasdinawa 7 ne suka yi shahada a wani mummunan hari da sojojin mamayar yahudawan sahayoniyya suka kai kan sansanin Jabaliya

Falasdinawa bakwai daga iyali daya ne suka yi shahada a daren jiya a wani mummunan hari da jirgin saman yakin sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi kan wani gida da ke sansanin ‘yan gudun hijira na Jabaliya da ke arewacin Zirin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, cibiyar yada labaran Falasdinu ta watsa rahoton cewa: Ma’aikatar tsaron farar hula a Gaza ta bayyana a wani sako da ta fitar a dandalin Telegram cewa: Falasdinawa 7 ne suka yi shahada yayin da wasu kuma suka jikkata sakamakon harin da jirgin saman yakin sojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya kai kan wani gida da ke sansanin Jabaliya da ke arewacin Zirin Gaza.

Haka nan Jiragen saman yakin haramtacciyar kasar Isra’ila sun yi ruwan bama-bamai a kan wani gidan zama na iyalan Ahmed da ke sansanin Jabaliya, lamarin da ya yi sanadin mutuwa da jikkatar wasu Falasdinawa da suka hada da kananan yara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments