Jakadan Falasdinu a MDD ya bayyana cewa; Dubbban Falasdinawa suna fuskantar kisan da HKI za ta yi musu saboda sun ki fita daga gidajensu a arewacin Gaza duk da laifukan yakin da HKI take tafkawa a kansu.
Sojojin HKI sun killace yankin arewacin Gaza tare da hana shigar da kayan abinci a cikinsa. Bugu da kari, sojojin HKI suna yi wa Falasdinawan kisan kiyashi saboda tilasta musu su fice daga cikin yankin.
Wakilin Falasdinu a MDD Riyadh Mansur ya ce: Dubban Falasdinawan suna fuskantar kisa saboda sun ki fita dafa gidajensu.”
Riyadh Mansur ya kuma ce “An killace Falasdianwa, ana kai musu hari, sannan kuma an jefa su cikin yunwa. Suna sane da cewa idan su ka fice daga gidajensu, to ba za a bari su koma ba.”
Jakadan na Falasdinawa a MDD ya yi mamakin cewa; Isra’ila wacce ta killace Falasdinawa ita ce ake bai wa kariya,amma Falasdinawa da ake azabtar da su, ba su da kowa sai Allah.”
Har ila yau, Riyadh Mansur ya ce Isra’ila ta shelanta yaki akan MDD da mu baki daya, ta kuma tsallake duk wani jan layi, kamar kuma yadda ta keta duk wata doka da ka’ida.
Kwanaki 25 kenan a jere da sojojin HKI a karkashin cikakken goyon bayan Amurka suke yi wa mazauna sansanin ‘yan hijira na Jabaliya kisan gilla.