Tarayyar Turai (EU) ta bayyana damuwarta da yadda kasar Turkiya a hukumanci a jiya Talata ta bada sanarwan cewa ta mika takardun bukatarta na zama mamba a kungiyar tattalin arziki ta Brics mai tasowa, duk da cewa ita mamba ce a kungiyar tsaro ta NATO.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Peter Stano kakakin kungiyar tarayyar Turai (EU) yana fadar haka a birnin Brussels, ya kuma kara da cewa, kasar turkiya tana da damar shiga duk wata kungiya da take so a duniya, amma kuma yakamata ta mutunta matsayinta na kasa wacce take son shiga kungiyar tarayyar Turai wato (EU). Don haka akwai bukatar ta tsara al-amuranta na harkokin wajen dai dai da yadda kasashen turai suke tafiya a kansu.
Kasar Turkiyya dai ta fara neman zama mamba a kungiyar tarayyar Turai (EU) ne tun shekara ta 2005 amma wasu kasashen kungiyar sun ki amincewa da hakan, saboda abinda suka kira matsalolin democradiyyarta.
A jiya ne shugaba Urdugan ya bada sanarwan cewa kasarsa ta mika takardunta na bukatar zama mamba a kungiyar BRICS .
A wani bangare kuma kasar Turkiyya ta ci gaba da hulda da kasar Rasha duk tare da cewa kungiyar tsaro ta NATO ce take jagorantar yakin da kasashen yamma suke yi da kasar Rasha.