Ecowas Ta Tura Sojoji Zuwa Jamhuriyar Benin Don Dakile Juyin Mulki

Kungiyar Habbaka Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka – Ecowas – ta sanar da tura rundunar ko-ta-kwana domin taimaka wa sojojin Jamhuriyar Benin wajen kakkabe sojojin

Kungiyar Habbaka Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka – Ecowas – ta sanar da tura rundunar ko-ta-kwana domin taimaka wa sojojin Jamhuriyar Benin wajen kakkabe sojojin da suka yi yunkurin juyin mulki.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar da yammacin jiya Lahadi, ta ce “Shugaban Ecowas, bisa ga amincewar shugabannin kasashen kungiyar ya amince da tura dakarun ko-ta-kwana zuwa Jamhuriyar Benin nan take.

Dakarun sun kunshi sojoji daga kasashen Najeriya da Saliyo da Cote d’Ivoire da kuma Ghana. Kuma za su taimaka wa gwamnati da kuma dakarun Jamhuriyar Benin wajen kare martabar kundin tsarin mulki da na kasar ta Benin.”

Rahotanni daga jamhurriyar Benin na nuni da cewa an kama sojoji da dama bayan wani yunƙurin juyin mulkin da bai yi nasara ba , Mutanen da aka kama sun haɗa da waɗanda ake zargi da jagorantar yunƙurin juyin mulkin.

A wata sanarwa da ya yi a gidan talabijin, ministan harkokin cikin gidan kasar Alassane Seidou, ya bayyana cewa dakarun kasar sun yi nasarar dakile yunkurin bayan da sojoji suka bayyana a gidan talabijin na kasar suna ikirarin cewa sun tsige shugaba Talon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted