Duniya Tana Bukatar Zaman Lafiya Da Yin Gyara A Kwamitin Tsaro

majalisar dinkin duniya tace duniya tana bukatar zaman lafiya da yin gyara a kwamitin tsaro

Babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Gutteres ya bayyana wajen taron koli na Asean cewa lallai duniya tana bukatar zaman lafiya , yana mai isharar game da yanayin da ake ciki a yankin gaza da yamen da gabashin asiya zuwa ukrani da kuma kasar Sudan, yace akwai bukatar kungiyoyin kasa da kasa su kare yancin dan adama acikin ko wanne irin yanayi

A cikin wani bayani da ya yi a yau litinin a wajen taron koli da ya hada kasashen gabashin asiya da kuma majalisar dinkin duniya karo na 49 da ake gudanar a manila babban barnin kasar philipihine  Guterres ya jinjinawa shugaban kasar filifin fardinand markus game da zaben da aka gudanar  a yankin bangsamuru.

Haka zalika babban sakataren yayi ishara game da tasirin rikicun da ke faruwa a yankin yace lallai na fahimci cewa tasirin rikicin rasha da ukrain a yankunanku,  da ma yanayin da ake ciki a tekun bahar maliya, da kuma tasirin rikice-rikice daban daban da ake yi a gabas ta tsakiya , da kuma barazanar da ake fuskanta na rufe mashigar hormuz da tekun bahar maliya  Gutteres ya jaddada cewa muna bukatar zaman lafiya a gaza da yamen da ma yankin gabas ta tsakiya da kuma ukrain da kasar Sudan dama yankunan dake kewaye da ita. daga karshe ya nuna cewa wannan shi ne karo na karshe da zai halarci taro tsakanin majalisar da kuma kungiyar Asean a matsayinsa na sakataren majalisar, amma duk da haka zai ci gaba da bibiyar makomar yankin da bin da ya shafe shi

a

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted