Duniya Na Ci Gaba Da Yin Allawadai Da Harin Isra’ila A Kan Iran

Kasashen Larabawa da dama kasashen duniya da dama sun yi tir da harin da yahudawan sahyuniya suka kai wa Iran, wanda ya nufi wasu sansanonin

Kasashen Larabawa da dama kasashen duniya da dama sun yi tir da harin da yahudawan sahyuniya suka kai wa Iran, wanda ya nufi wasu sansanonin soji a lardunan Tehran, Ilam da Khuzestan da jijjifin safiyar wannan Asabar.

Saudiyya, UAE, Yemen, Iraki, Syria, Kuwait, Qatar, Jordan, Oman, Lebanon da Aljeriya duk sun fitar da bayanai na yin tir da Allah wadai da zaluncin yahudawan sahyoniya da kuma wuce gonad a iri a kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya ta tabbatar da cewa, harin ya kasance cin zarafi ne ga kasa mai cikakken ci gashin kai da ‘yanci, sannan kuma hakan yin hawan kawara ne a kan dokoki da da ka’idoji na kasa da kasa.

Masarautar Saudiyya ta jaddada matsayar ta na adawa da ci gaba da tabarbarewar al’amura a yankin da kuma fadada rikicin da ke barazana ga tsaro da zaman lafiyar kasashen yankin. Sanarwar ta ce: “Muna kira ga dukkan bangarorin da su yi iyakacin kokarinsu wajen kaucewa duk wani abu da zai kara ta’azzarawa da rura wutar tashin hankali a yankin.”

A nata bangaren, ma’aikatar harkokin wajen kasar Oman ta yi Allah wadai da kakkausar murya kan matakin da Haramtacciyar kasar Isra’ila ta dauka na kai hari kan Iran, wanda yake a matsayin keta hurumi ne ga kasar Iran da kuma dokokin kasa da kasa, sannan kuma kasar ta yi kira ga Haramtacciyar Kasar Isra’ila da ta kawo karshen irin wadannan ayyuka na keta hurumin kasashe masu ‘yanci.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments