Search
Close this search box.

Donald Trump Ya Bukaci Hanzarta Murkushe Falasdinawa Tare Da Adawa Da Tsagaita Bude Wuta

Donald Trump ya bukaci Netanyahu ya gaggauta samun nasara a Gaza kuma yana da burin ganin an fadada haramtacciyar kasar Isra’ila Dan takarar shugabancin Amurka

Donald Trump ya bukaci Netanyahu ya gaggauta samun nasara a Gaza kuma yana da burin ganin an fadada haramtacciyar kasar Isra’ila

Dan takarar shugabancin Amurka a karkashin jam’iyyar Republican Donald Trump, ya ce ya bukaci Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu da ya kawo karshen yakin da yahudawan sahayoniyya suka kaddamar a Gaza cikin gaggawa, amma kuma ya soki kiran tsagaita bude wuta.

Trump ya shaida wa manema labarai yayin wani taron manema labarai a jiya Alhamis cewa: Benjamin Netanyahu ya san abin da yake yi, kuma Trump ya ce ya karfafa masa gwiwa da ya kawo karshen yakin Gaza cikin gaggawa, bisa nasarar yahudawan sahayoniyya, sannan Trump ya soki kiraye-kirayen tsagaita bude wuta ba tare da an murkushen Falasdinawa ba.

Trump ya yi wannan magana ce a ganawarsa da Netanyahu a gidansa a karshen watan Yuli, lokacin da Netanyahu ya ziyarci Amurka a wancan lokacin, sannan Netanyahu ya kuma gana da Shugaba Joe Biden da mataimakiyarsa da take ‘yar takarar shugaban kasa na jam’iyyar Democrat Kamala Harris.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments