Daruruwan Yahudawa ‘Yan Share Wuri Zauna Sun Kutsa Masallacin Kudus

Kamfanin dillancin labarun “Irna” ya  nakalto cewa; A yau Lahadi kadai,yahudawan sahayoniya da sun kai 500 sun kutsa cikin harabar masallacin Kudus a daidai lokacin

Kamfanin dillancin labarun “Irna” ya  nakalto cewa; A yau Lahadi kadai,yahudawan sahayoniya da sun kai 500 sun kutsa cikin harabar masallacin Kudus a daidai lokacin da suke yin bikin Edinsu na addini na tunawa da lokacin dimuwar Yahudwa a saharar Sina.

A jiya Lahadi ma dai ministan tsaron cikin gida na HKI Itamar Bin Gvir tare da wasu ‘yan share wuri zauna din sun kutsa cikin masallacin na Kudus da yin abubuwa na tsokanar musulmi.

Tun tuni yahudawan sahayoniyar suke kokarin samun damar da za su rushe masallacin kudus da zummar gina wurin bautarsu na yahudawa a bagirensa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments