Dakarun Yemen sun kaddamar da hari kan katafaren jirgin ruwa na MEGALOPOLIS

A yammacin jiya Juma’a kakakin rundunar sojojin kasar Yemen Birgediya Janar Yahya Saree ya sanar da cewa, sojojin saman kasar ta Yemen sun kai hari

A yammacin jiya Juma’a kakakin rundunar sojojin kasar Yemen Birgediya Janar Yahya Saree ya sanar da cewa, sojojin saman kasar ta Yemen sun kai hari kan jirgin ruwan MEGALOPOLIS da ke cikin tekun Larabawa ta hanyar amfani da jirage marasa matuka, inda ya tabbatar da cewa an cimma manufar aikin.

Saree ya bayyana cewa harin da aka kaiwa jirgin ya zo ne bayan da kamfaninsa ya sabawa matakin hana shiga tashar jiragen ruwa ta Falasdinu da Isra’ila ta mamaye. Haramcin ya zo ne a matsayin nuna goyon baya ga al’ummar Palasdinu da na Labanon.

Saree ya kuma jinjinawa mayakan ‘yan gwagwarmaya a Gaza da Lebanon, yana mai jaddada cewa shahadar babban jigo, shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas, Yahya Sinwar, za ta kara azamar gwagwarmaya da zaluncin Isra’ila ne kawai, da karfafa gwiwar duk wasu ‘yantattu a duniya, wajen tunkarar zalunci da babakere na yahudawan sahyuniya har zuwa samun nasara.

Ya kuma kara jaddada cewa, a yayin da dakarun kasar Yemen ke shiga shekara ta biyu na goyon bayansu ga gwagwarmayar al’ummar Gaza da ke fuskantar kisan kare dangi, a daya bangaren kuma dakarun na Yemen na suna nan suna ci gaba da kokarin ganin an tabbatar da dokar hana zirga-zirgar jiragen ruwa da ke kai dauki ga haramtacciyar kasar Isra’ila, tare da kai hari kan dukkan jiragen ruwa da ke da alaka da su, da ke kan hanyarsu zuwa Falastinu da yahudawa suka mamaye.

Saree ya tabbatar da ci gaba da kai hari kan Isra’ila da makamai masu linzami da jirage marasa matuka, ya kuma jaddada cewa wadannan ayyuka ba za su gushe ba har sai an kawo karshen hare-hare a kan Gaza da kasar Labanon.

A nasa bangaren Shugaban kungiyar Ansar Allah ta kasar Yemen, Abdul-Malik al-Houthi, ya bayyana ta’aziyyarsa ga iyalan shugaban Hamas Yahya Sinwar, da ofishin siyasa na kungiyar, dadakarun al-Qassam Brigades, da al’ummar Palastinu, da ma daukacin al’ummar musulmin duniya, biyo bayan shahadarsa a hannun sojojin yahudawan sahyuniya, inda Alhouthi ya ce ya samu matsayi mafi daraja da daukaka na shahada a tafarkin gaskiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments