Rahotonni sun bayyana cewa: Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces sun aiwatar da wani sabon kisan kiyashi kan fararen hula a birnin Al-Qatana da ke arewacin jihar White Nile a Sudan, wanda ya yi sanadin mutuwar daruruwan fararen hula tare da tarwatsa al’ummar yankin, inda suka fantsama zuwa gudun hijira.
Ma’aikatar harkokin wajen Sudan ta tabbatar da cewa: Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces sun gudanar da wani kisan kiyashi da ya yi sanadin mutuwar mutane 433 a kauyukan birnin Al-Qatana na jihar White Nile.
Ma’aikatar harkokin wajen Sudan a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce: Dakarun kai daukin gaggawa sun yi amfani da salon da suka saba yi na daukar fansa kan fararen hula da ba su dauke da makamai a kauyuka da kananan garuruwa bayan da suka sha kashi a hannun sojojin Sudan.