Dakarun Kai Daukin Gaggawa Sun Kashe Fararen Hula Kusan 300 A Hare-Haren Baya-Bayan Nan A Sudan

Ana gwabza kazamin fada a Sudan, inda dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces suka kashe fararen hula kusan 300 A tsakiyar bala’in Sudan,

Ana gwabza kazamin fada a Sudan, inda dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces suka kashe fararen hula kusan 300

A tsakiyar bala’in Sudan, ana ci gaba da gwabza kazamin fada tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa, a daidai lokacin da ake fama da munanan ayyukan jin kai da ke ba da mummunan hoto kan makomar kasar.

A yammacin jihar Kordofan, sojojin kasar Sudan sun sanar da janyewa daga birnin Nahud, bayan kazamin fada da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces, wadanda suka sanar da kwace iko da birnin da kuma hedikwatar Brigade ta sha takwas, baya ga birnin Al-Khawi.

Yayin da ake ci gaba da gwabza fada, gwamnatin Sudan ta zargi dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces da aikata munanan laifuka kan fararen hula a birnin Nahud, da suka hada da kisan kai, sace-sacen dukiya da lalata cibiyoyi. Ta kuma sha alwashin hukunta wadanda ke da hannu a aikata wadannan muggan laifuka da kuma kasashen da ke tallafa musu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments