Sudan: Dakarun RSF Sun Kashe Fararen Hula 14 Tare Da Jikkata Wasu

Fararen hula 14 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata a wani hari da dakarun kai daukin gaggawa suka kai El Fasher

Fararen hula 14 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata a wani hari da dakarun kai daukin gaggawa suka kai El Fasher na Sudan

Wata kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasar Sudan ta sanar da cewa:  kungiyar Rapid Support Forces ta kasar Sudan ta Dakarun kai daukin gaggawa ta kashe akalla fararen hula 14 a lokacin da take yunkurin tserewa wani yanki da aka killace a yankin Darfur, bayan shafe sama da watanni 27 ana yaki tsakanin dakarun ‘yan tawaye da sojojin Sudan.

Kungiyar lauyoyin gaggawa da ke tattara bayanan cin zarafi da aka yi a yakin, ta kuma watsa rahoton cewa: “An samu raunuka da dama, kana an kama wasu fararen hula da ba a san adadinsu ba a harin da mayakan kungiyar Rapid Support Forces suka kai hari kan kauyen Qarni da ke arewa maso yammacin birnin El Fasher da ke yammacin Darfur da aka killace a ranar Asabar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments