Matainakin shugaban kasar kasar Iran na farko Mohammad Reza Aref ya bayyana cewa, daukewa Iran takunkuman zalunci wadanda kasashen yamma suka dora mata na daga cikin asalin hakkin kasar da aka tauye.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Aref yana fadar haka a jiya Asabar, ya kuma kara da cewa, kasar Iran ba zata manta da hakkin kasar wanda Amurka ta take tun farkon nasarar juyin juya halin kasar shekaru 46 zuwa yanzu ba, amma duk da haka sun bata damar tattaunawa. Yace: Muna son mu nunawa duniya kan cewa har yanzun muna hakuri, amma ba zamu taba manta da zaluncin da aka yi mana ba. Mataimakin shugaban yana maganar ficewar kasar Amurka daga yarjeniyar JCPOA da kuma dorawa kasar takunkuman tattalin arziki mafi muni da nufin kifar da gwamnatin kasar. Yace dukkan takunkuman tattalin arzikin da gwamnatocin kasar Amurka ta dorawa kasar tun bayan nasarar juyin juya halin kasar shekaru 46 da suka gabata basa bisa ka’ida. Mataimakin shugaban kasar yana fadar haka ne bayan da ministan harkokin wajen kasar Abbas Aragchi ya kammala zagaye na farko na tattaunawa ba kai tsaye ba kan shirin makamacin Nukliya na kasar da tokwaransa na kasar Amurka Steve Witkoff a kasar Omman tare da ministan harkokin wajen kasar Omman Badr Hamad Al-Busaidi a matsayin mai shiga tsakani.
Iran Ta Godewa Omman Da Shiryawa Da Kuma Gudanar Da Tattaunawa Tsakanin Amurka Da Iran