Cikan Kwanaki 247 Da Fara Kai Hare-Haren Wuce Gona Da Iri Kan Zirin Gaza Na Falasdinu

Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta cika rana ta 247 a yakin da take kaddamarwa kan yankin Zirin Gaza Munanan hare-haren wuce gona da iri da

Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta cika rana ta 247 a yakin da take kaddamarwa kan yankin Zirin Gaza

Munanan hare-haren wuce gona da iri da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kai wa Zirin Gaza ya shiga kwana na 247, a daidai lokacin da ake ci gaba da gudanar da zanga-zanga a biranen Washington na Amurka da London na Birtaniya, inda jama’a suke yin tir da kisan gillar da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi a kullum rana a Falasdinu tare da neman kawo karshen yakin.

Kisan kiyashi na baya-bayan nan dai shi ne wani mummunan harin wuce gona da iri da sojojin gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai a ranar Asabar kan sansanin Nuseirat da ke tsakiyar Zirin Gaza, domin neman kubutar da wasu fursunonin yahudawan sahayoniyya hudu da ake tsare da su a Gaza. Sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat da lungunansa sun rikide zuwa wani fagen yaki a ranar Asabar da ta gabata, inda jiragen saman yakin sojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka din ga yin luguden wuta kan sansanin tare da harba bama-bamai da kuma luguden manyan bindigogi gami da kutsen sojojin yahudawan sahayoniyya na musamman cikin sansanin lamarin da ya wurga Falasdinawa a sansanin cikin firgici mai tsanani.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments