Cibiyar kula da lafiya ta Nasser Medical Complex da ke Gaza ya bayyana cewa: Yara 5,500 ne ke bukatar agajin gaggawa a kasashen waje
Daraktan cibiyar kula da lafiya ta Al-Shifa da ke Gaza ya ce: Babu wani agajin jinya da ya shiga zirin Gaza duk da cewa an shafe sa’o’i 72 tsagaita bude wuta.
Ya kara da cewa: Mutane 170,000 marasa lafiya da kuma wadanda suka jikkata na bukatar tafiya cikin gaggawa zuwa wajen Gaza domin neman magani.
Al-Nasser Medical Complex ya kuma ce: Yara 5,500 na bukatar magani a wajen Gaza. Daraktan asibitin yara na Nasser Medical Complex, Dr. Ahmed Al-Farra, ya bayyana cewa, akwai yara 5,500 a zirin Gaza da ke bukatar agajin gaggawa a wajen yankin saboda tsananin karancin magunguna da kuma ci gaba da tabarbarewar yanayin kiwon lafiya.
A nata bangaren, Nour Al-Saqa, mai kula da harkokin yada labarai na kungiyar likitocin da ke yankin zirin Gaza, ta ce sama da mutane 170,000 da suka jikkata a zirin Gaza na bukatar kulawar gaggawa.
Yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta fara aiki tun ranar Juma’a. A matakin farko, yarjejeniyar ta tanadi shigar da kusan tireloli 600 na kayan agajin gaggawa a kowace rana. Sai dai wasu kananan motoci ne kawai aka ba su izinin shiga, kuma har yanzu ba a kai agajin jinya a zirin Gaza ba.