Gwamnatin kasar China ta bada sanarwan kara kodaden fito kan kayakin Amurka wadanda suke shigowa kasa har na kasha 80% sannan a shirye take ta ci gaba da yakin kasuwanci da gwamnatin shugaba Trump har zuwa karshe.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jami’an gwamnatin kasar China na fadar haka a yau Laraba sun kuma kara da cewa, idan gwamnatin Trump bata dakatar da wannan yakin kasuwanci ba to kasar China tana da hanyoyi da dama wadanda zata ci gaba da wannan yakin har zuwa karshe.
Kafin haka dai gwamnatin shugaba Trump ta karawa kayakan kasar China masu shigowa Amurka kudaden fito daga kashe 34% zuwa kasha 104 % kuma a yau Laraba ne dokar karin zai fara aiki. Amma karin da gwamnatin kasar China ta yi zai fara aiki ne a ranar 10 ga watan Afrilu da muke ciki wato gobe Alhamis.
A ranar laraban da ta gabata ce shugaban kasar Amurka Donal Trump ya kara kudaden fito ga kasashen duniya da dama daga cikin har da kasar China wacce ta maida martani bayan kwanaki biyu da kwatankwacin abinda Amurka ta kara mata.