Shugaban kasar Cape Verde, José Maria Neves, ya sake lashe zaben shugabancin kasar.
Sakamakon farko, da aka fitar a bisa kashi 98% na kuri’un da aka kirga, shugaban mai ci ya sami kashi 63.8% na kuri’un, a yayin da babbar abokiyar hamayyarsa, Joana Rosa Amado ta samu kashi 31.5%.
An sake zaben José Maria a wa’adi na biyu bayan nasararsa ta farko a 2021, ya kuma yi alkawarin zama shugaban dukkan ‘yan Cape Verde, ba tare da la’akari da zabinsu na siyasa ba.
Duk da ci gaban tattalin arziki da yawon bude ido ke haifarwa, Cape Verde na ci gaba da fuskantar kalubale da dama na zamantakewa.
Tsarin rayuwa, farashin mai, rashin aikin yi ga matasa, da rashin daidaito suna daga cikin manyan abubuwan da ke damun jama’a.
José Maria Neves ya yi alkawarin samar da tattaunawa tsakanin jam’iyyun siyasa don samar da samun gidaje, kiwon lafiya, da ilimi, tare da karfafa samar da ayyukan yi da karin albashi.
Cape Verde, wacce take a Tekun Atlantika, a gefen gabar tekun Senegal, tana da yawan jama’a kusan rabin miliyan.