Bullar Tashe-Tashen Hankula A Haramtacciyar Kasar Isra’ila Musamman Barazana Kan Jami’ai

Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi furuci da cewa: Ana barazanar yin fyade ga matarsa a matsayin ramakon gayya kansa Fira ministan gwamnatin

Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi furuci da cewa: Ana barazanar yin fyade ga matarsa a matsayin ramakon gayya kansa

Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana fargabar bullar kashe-kashen gilla a haramtacciyar kasar Isra’ila, yana mai cewa ana kokarin tayar da tarzoma a cikin haramtacciyar kasar Isra’ila musamman tun bayan yunkurin hallaka tsohon shugaban Amurka Donald Trump a lokacin da yake jawabi a wani taron yakin neman zabe a lokacin gangami magoya bayansa.

A wata hira da ya yi da gidan talabijin na 14 na haramtacciyar kasar Isra’ila Netanyahu ya ce: Akwai makircin da akekulla na tunzura jama’a domin gudanar da kashe-kashen gilla kan zababbun jami’ai a haramtacciyar kasar Isra’ila, kuma hakan na iya kaiwa ga fira minista da iyalansa, yana mai jaddada cewa yana fuskantar barazana ba dare ba rana. kuma akwai wadanda suke yi masa kururuwa cewa shi maci amana ne kuma mai kisan kai ne.

Ya ci gaba da cewa: Ba shi kadai ba, barazanar ta hada da iyalinsa, Yana mai zargin bangarorin ‘yan adawa da hannu a rurata wutar rikici a haramtacciyar kasar Isra’ila.

Yana mai jaddada cewa: Matarsa ​​Sarah tana fuskantar barazanar fyade da cin mutunci, da zage-zage ba dare ba rana daga iyalan yahudawa da ‘yan uwansu suka halaka da wadanda ‘yan uwansu suke hannun Falasdina a matsayin fursunonin yaki a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments