Search
Close this search box.

Brazil ta kirayi jakadanta da ke Tel Aviv sakamakon yakin Isra’ila a Gaza

Wata majiyar diflomasiyya ta sanar da cewa, Brazil ta kira jakadanta da ke  Isra’ila, lamarin da ya kara tada jijiyoyin wuya a tsakanin kasashen biyu

Wata majiyar diflomasiyya ta sanar da cewa, Brazil ta kira jakadanta da ke  Isra’ila, lamarin da ya kara tada jijiyoyin wuya a tsakanin kasashen biyu sakamakon yakin da Isra’ila ke yi a Gaza.

Da farko dai an gayyaci jakada Frederico Mayer don tuntubar gwamnatinsa, bayan da Brazil da Isra’ila suka yi musayen kalamai masu zafi a watan Fabrairu kan rikicin Gaza. Wata majiyar diflomasiyya ta shaida cewa “babu wani sharadi na komawar jakadan zuwa Isra’ila.”

Tun da farko, Celso Amorim, mai ba da shawara na musamman ga shugaban Brazil Luiz Inacio Lula da Silva, ya sanar da cewa jakadan ba zai koma Tel Aviv ba.

Jaridar Folha de São Paulo ta Brazil ta rawaito cewa Lula da Silva ya gayyaci jakadan kasarsa da ke Tel Aviv domin tattaunawa, bayan da ministan harkokin wajen Isra’ila, Isra’il Katz ya bayyana cewa shugaban na Brazil mutum ne da ba a sonsa.

Lula da Silva ya dauki abin da ke faruwa a zirin Gaza a matsayin “kisan kare dangi,” kuma ya kwatanta shi da irin ta’asar da yahudawa ke da’awar cewa Hitler ya yi musu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments