Brazil: Al’ummun Yankunan Karkara Na Amazon Sun Yi Gangami A Wurin Taron MDD Akan Muhalli

Masu gangamin da adadinsu ya kai 100 sun tsaya a gaban babbar kofar shiga wurin taron kare muhalli na MDD da aka bude a garin

Masu gangamin da adadinsu ya kai 100 sun tsaya a gaban babbar kofar shiga wurin taron kare muhalli na MDD da aka bude a garin Belem dake yankin Amazon na Brazil.

Sojojin kasar Brazil sun bai wa masu gangamin kariya, tare da kaucewa yin taho mu gama saboda su sami damar isar da sakonsu akan abinda yake faruwa na sauyin yanayi da shi ne jigon taron.

Wata mace da ta fito daga Munduruku daga jahar Par, ta fadawa manema labaru cewa: “Mun zo nan wurin ne tun kwanaki da yawa, kuma muna son a ji muryoyinmu ne. Muna son zama ne domin yin taattaunawa aka abinda ya shafi sauyin yanayi.”

Al’ummun karkara, wadanda sauyin yanayi yake shafa kai tsaye, suna yin korafin cewa, ba a jin muryoyinsu a yayin taruka irin wadannan masu alaka da sauyin yanayi.

Kabilun da su ka yi gangamin a wurin taron na Belem sun zargi gwamnatin kasar ta Brazil a karkashin shugaba Lula da yin wata doka akan tsaga hanyoyin ruwa a cikin yankin da za su yi barna akan muhalli.

Korap wacce ta yi magana da sunan kabilun yankin, ta bayyana cewa:

“A duk lokacin da mahukunta su ka hako man fetur, suna yi wa kawukansu murna. Idan sun amince da hako ma’adanai suna tafa wa kawukansu. “

Haka nan kuma ta kara da cewa: Ba a shirye muke mu yi musayar kasarmu da kudi ba… Abinda muke so shi ne girmamawa.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments