Search
Close this search box.

Borrell, Ya Bukaci, Sanya Takunkumi Kan Masu Tsattsauran Ra’ayin Yahudawa

Babban jami’in diflomasiyyar Tarayyar Turai Josep Borrell ya ce zai ba da shawarar sanya takunkumi kan masu tsauttsauran ra’ayin yahudawa sakamakon wani mummunan harin da

Babban jami’in diflomasiyyar Tarayyar Turai Josep Borrell ya ce zai ba da shawarar sanya takunkumi kan masu tsauttsauran ra’ayin yahudawa sakamakon wani mummunan harin da aka kai a wani kauye da ke gabar yammacin kogin Jordan da aka mamaye.

Kusan “Kowace rana, ba tare da wani dalili ba, mazauna yahudawan suna haifar da tashin hankali a Yammacin Kogin Jordan, wanda hakan ke tarnaki ga duk wata dama ta samar da zaman lafiya,” inji Borrell a shafinsa a kan X ranar Juma’a.

“Dole ne gwamnatin Isra’ila ta dakatar da wadannan ayyukan da ba za a amince da su ba,” in ji shi, yana mai shan alwashin “tabbatar da shawarwarin takunkumin EU kan masu tayar da hankali, ciki har da wasu mambobin gwamnatin Isra’ila”.

Tunda farko dai ma’aikatar harkokin wajen Falasdinu ta bayyana abin da ta kira ‘ta’addanci da kasa ta shirya’ sakamakon wani hari da masu tsattsauran ra’ayin Yahudawa ‘yan kama-wuri-zauna suka kai a kauyen dake gabar yamma da kogin Jordan inda aka kashe Bafalasdine guda.

Wani mazaunin garin Jit ya ce “Masu tsattsauran ra’ayin da suka rufe fuskokinsu kuma sanye da kayan sojoji dauke da kulake sun cinna wa wani gida wuta sannan kuma suka kona wadansu motoci a garin, lamarin da kasashen duniya da kungiyoyi da dama sukayi tir da shi.

Shugabanin Falasdinawa sun yi Allah-wadai da harin, yayin da Shi kuwa Firaiminista Benyamin Netanyahu ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici.

Fadar gwamnatin Amurka, White House ta soki hukumomin Isra’ila saboda kasa kai dauki a kan lokaci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments