Boko Haram Ta Kashe Mutane Akalla 85 A Arewaci Maso Gabacin Tarayyar Najeriya

Mayakan kungiyar boko Haram a arewa maso gabacin tarayyar Najeriya sun kashe mutane 85 a karamar hukumar Tarmuwa a jihar Yobe na kasar. Kamfanin dillancin

Mayakan kungiyar boko Haram a arewa maso gabacin tarayyar Najeriya sun kashe mutane 85 a karamar hukumar Tarmuwa a jihar Yobe na kasar.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa kan cewa mafi yawan wadanda aka kashen manoma ne a garin Wafa na karamar hukumar Tarmuwa na jihar Yobe.

Kafin haka dai mayakan na boko haram sun kashe mutane uku yan shi’a daga kungiyar IMN a garin Dambua na Jihar sannan suka kashe wasu a a wannan makon a wasu wurare.

Labarin ya kara da cewa shugaban limaman jumma na jihar ne Sheikh Hudu Muhammad Yusuf ne ya sallaci gawakin wadanda aka kashen.

Sannan sarkin Jajere Alhaji Mai Buba Isa Mashio ya ci gaba da karban ta’ziyyar kissan mutanen.

Kungiyar Boko haram dai ta fara yakar gwamnatin tarayyar Nageriya ne tun shekata ta 2009, kuma ya zuwa yanzu an kashe mutane kimani 50,000 a yayinda wasu miliyon  biyu da rabi suka kauracewa gidajensu a arewacin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments