Ministan cikin gida na HKI Ben-Gvir ya bukaci gwamnatin HKI ta kwace yankin zirin gaza daga hannun Falasdinawa, ta kuma shigo da baki yahudawa daga kasashen waje wadanda zasu zauna a yankin, don a huta da Falasdinawa a yankin gaba daya.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Gvir yana fadar haka a shafinsa na X jim kadan bayan kissan kare dangi wanda jiragen yakin HKI suka yi wa falasdinawa fiye da 150 a makarantar ta’bi’ina a gaza a jiya Asabar da safe a birnin gaza da kuma raunata wasu daruruwa.
Ben Gvir ya bukaci a dakatar da shiguwar abinci a gaza ko da hakan zai sa Falasdinawa miliyon biyu su mutu saboda yunwa. Sannan ya kara jaddada bukatar a hana kome shigowa Gaza sai idan Falasdinawa sun saki fursinonin yaki wadanda kungiyar Hamas take tsare da su fiye da watanni 10 da suka gabata.
Har’ila yau ministan kudi na HKI Bezalel Smotrich ya bukaci gwamnatin Natanyahu ta yi duk abinda zata yi don kwace Gaza ko da hakan zai kai ga kisan dukkan Falasdinawa a Gaza. Ya ce hakan shi ne dai dai kuma ya halatta.