Bayan Kalubalantar Ra’ayin Amurka Kan Gaza Trump Ya Ce Furucinsa Shawara Ce Kawai

Shugaban kasar Amurka ya bayyana cewa: Shirinsa kan Zirin Gaza yana da kyau, amma ba zai tilasta aiwatar da shi ba, sai dai zai ci

Shugaban kasar Amurka ya bayyana cewa: Shirinsa kan Zirin Gaza yana da kyau, amma ba zai tilasta aiwatar da shi ba, sai dai zai ci gaba da ba da shawara kawai

An gudanar da wani zaman taron koli na kasashen Larabawa a kasar Saudiyya, inda aka tattauna Shirin kalubalantar kudirin shugaban Amurka Donald Trump dangane da Gaza.

Taron tuntuba da aka gudanar bisa gayyatar yarima mai jiran gado na Saudiyya; Zaman ya tattauna ra’ayoyi kan kokarin hadin gwiwa na goyon bayan al’ummar Falasdinu.

Kamfanin dillancin labaran Saudiyya ya watsa rahoton cewa: An gudanar da taron na yau da kullun tare da halartar sarkin kasar Jordan, shugaban kasar Masar, da kuma kasashen Larabawan yankin Tekun Fasha, in ban da masarautar Oman, inda suka jaddada goyon bayan zaman shugabannin kungiyar na birnin Alkahira da zai karbar bakwancin zaman taron gaggawa na kungiyar kasashen Larabawa a farkon wata mai zuwa.

A nata bangaren, majiyoyin da aka sanar sun ce taron ya tattauna wata shawara ta Masar don mayar da martani ga shirin Trump na tilastawa Falasdinawa gudun hijira, wanda zai iya hada tallafin kudade da suka kai dala biliyan ashirin cikin shekaru uku.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments