Bashar al-Assad, Ya Je Iran, Domin Isar Da Ta’aziyya

Jagoran juyin juya halin mulinci na Iran, ya gana da Shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad, wanda ya ziyarci kasar domin isar da sakon ta’aziyarsa game

Jagoran juyin juya halin mulinci na Iran, ya gana da Shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad, wanda ya ziyarci kasar domin isar da sakon ta’aziyarsa game da rasuwar shugaba tsohon shugaba Ibrahim Ra’isi da mukarabansa a hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu.

Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya mika godiyarsa ga shugaba Bashar al-Assad kan ziyararsa a birnin Tehran domin jajantawa al’ummar Iran.

Jagoran ya jaddada muhimmancin karfafa alaka tsakanin Iran da Syria, wadanda su ne ginshikai guda biyu na bangaren tsayin daka,

ya kuma bayyana irin rawar da shugaba Raisi da Amir Abdollahian suka taka wajen inganta alaka tsakanin Iran da Siriya.

Yayin da yake ishara da matsin lamba na siyasa da tattalin arziki da Amurka da Turai suke yi kan Iran da Siriya, Jagoran ya ce kamata ya yi a shawo kan wadannan matakan ta fuskar karfafawa hadin gwiwa.

A nasa bangare Shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad ya mika ta’aziyyarsa ga Jagoran juyin juya halin Musulunci da gwamnati da kuma al’ummar Iran kan babban rishin da kasar ta yi na Shugaba Ra’isi da AmirAbdollahian wadanda ya ce sun kasance a sahun gaba wajen tsayin daka da da kare tafarkin da kasar ke kan shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments