Akalla mutane 39 sun mutu sakamakon nutsewar kwale-kwalen bakin haure a gabar tekun Senegal
Wani ƙaramin jirgin ruwa dauke da bakin haure ya nutse a arewa maso yammacin Senegal, inda ya kashe akalla mutane 35 a cikin mummunan bala’in da ya faru a kan hanyar Tekun Atlantika mai hatsari daga Afirka zuwa Turai, kamar yadda hukumar agajin gaggawa ta shaida wa kamfanindillancin labaran AFP a ranar Lahadi.
A kan wannan hanyar, dubban mutane sun mutu a cikin ‘yan shekarun nan yayin da suke ƙoƙarin isa Tsibirin Canary na Spain daga yammacin Afirka.
Wata sanarwa ta farko daga ma’aikatar harkokin cikin gida ta Senegal ta ce an gano gawawwaki 21 kuma mutum ɗaya ne kawai ya tsira bayan nutsewar jirgin, amma waɗannan alkaluman na wucin gadi ne yayin da ake ci gaba da neman jirgin.