Akalla mutane 20 ne suka mutu a karshen mako sakamakon kifewar wasu kwale-kwalen da suke ciki a tsuburin Crete, yayinda suke shirin tsallakawa zuwa kasar Girka ta teku, kamar yadda mahukuntan Tarayyar Turai suka tabbatar.
Zuwa yanzu dai an gano gawarwaki 8 a cikin kwale-kwale guda sai kuma wasu 12 da suke cikin dayan , yayinda kuma aka ceto wasu mutan 40 da ransu .
Jami’an ƴan sandan da ke kula da gabar teku sun kaddamar da aikin ceto na gaggawa tun ranar Asabar din da ta gabata, ko da yake aikin nasu na gamuwa da tangarda sakamakon iska da guguwa da ke murda ruwan teku.
Bayanai sun ce mutane 28 cikin wadanda aka ceto da kuma guda da ya rasu yan asalin kasar Sudan ne sai kuma mutum 7 da ba’a bayyana asalinsu ba. Tsuburin Crete na zama wani tudun mun tsira ga baki ƴan gudun hijira da ke fatan tsallakawa turai daga nahiyar Afrika, musamman kasar Libya, zuwa Girka.