Baka’i: Babu Wani Dalili Da Zai Sa Kungiyoyin Kasa Da Kasa Yin Shiru Akan Laifukan HKI

 Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’ila Baka’i ya bayyana cewa; Harin da HKI ta kai wa asibitin Kamal Adwan babban laifi ne wanda ya munana,

 Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’ila Baka’i ya bayyana cewa; Harin da HKI ta kai wa asibitin Kamal Adwan babban laifi ne wanda ya munana, don haka babu dalilin da zai sa kungiyoyin kasa da kasa su yi shiru akansa.

Isma’il Baka’i ya yi suka da kakkausar murya akan yadda sojojin mamayar HKI su ka kai wa asibitin da kuma kone shi, shi ne sabon laifin yakin da HKI ta tafka, da kuma laifi akan bil’adama sannan kuma keta dokokin kasa da kasa a fili.

Baka’i ya kuma ce; Manufar aikata wannan laifin shi ne rusa duk wasu cibiyoyin kiwon lafiya a Gaza baki daya, da haka kananan yara da mata da maza da su ka jikkata sanadiyyar yaki, samun magani.

Haka nan kuma ya ce, Asibitin Kamal Adawan shi ne cibiyar kiwon lafiya ta karshe a arewacin  Gaza.

Bugu da kari kakakin ma’aikatar harkokin wajen ta Iran ta ce, shirun da kungiyoyin kasa da kasa su ka yi akan wannan batun ba shi da halartaccen dalili,kuma wannan irin shirun da ake yi ne yake zama tarayya a cikin laifi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments