Baghiri Kani Da Fidan Sun Tattauna Karin Dankon Zumunci Da Raya Kasashen Yankin Asia Ta Kudu

Ministocin harkokin waje na kasashen Iran ta turkiya sun tattauna dangane da kara kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu da kuma raya kasashen yankin asiya ta

Ministocin harkokin waje na kasashen Iran ta turkiya sun tattauna dangane da kara kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu da kuma raya kasashen yankin asiya ta kusu a gefen taronkasashen musulmi 8 da D8 ta raya tattalin arziki a birnin istambul na kasar Turkiya.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto makaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran wanda yake ziyarar aiki a kasar Turkiya tun ranar jumma’a yana cewa kasashen D8 sun amince kan daukar matakai masu yawa kan HKI saboda ta’asan da take aikatawa a gaza.

Kani ya bayyana cewa HKI makiyi ce ga kasashen Iran da Turkiyya kuma hadin kai tsakanin kasashen biyu zai bunkasa tattalin arzikin kasashen yankin har ila yau zai kara kyautata harkokin tsaro a kasashen yankin kudancin Asia.

A jawabin da ya gabatar a taron ministocin harkokin wajen kasashen D8 ya bukaci kasashen su dauki HKI a matsayin gwamnatin wariya , Sannan akwai bukatar a raya kudurin MDD mai lamba 3379 wanda yake Magana a kan wannan lamarin.

Sannan daga karshe ya buakaci kasashen su yi aiki tare don warware matsalolin Falasdinawa saboda hadin kai a tsakaninsu da kuma dinke dukkan barakar da ka iya tasowa a tsakaninsu.

A Nashi bangaren  ministan harkokin wajen kasar Turkiya ya yabawa kasar Iran kan taimakon da take bawa al-ummar falasdinu da kuma kokarinta na hada kan kasashen yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments