Hukumomi a India sun ce da yiwa a samu wanda ya tsira daga hatsarin jirgin samanAir India da ya faru a yau Alhamis.
Jirgin samfarin Boeing 787 Dreamliner wanda ya tashi Ahmedabad zuwa birnin Landan ya yi hatsari jim kadan bayan tashinsa dauke da fasinjoji 242 da ma’aikatan jirgin inji kamfanin air India.
Bayanan farko da kamfanin na Indiya ya fitar sun ce akwai, Indiyawa 169, ‘yan Burtaniya 53 da, ‘yan Portugal 7 sai dan Canada guda a cikin jirgin. Kuma babu wanda ya tsira, a cewar shugaban ‘yan sandan Ahmedabad.
Hukumomin India da na Ingila da Portigal duk sun jajanta game da mummunan hatsarin.
Jami’an kashe gobara a arewa maso yammacin Indiya tun da farko sun shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa wani jirgin sama ya fado a filin jirgin.
Hotunan farko da aka watsa a gidajen talabijin na Indiya sun nuna wani jirgin sama yana shawagi a wata unguwa, kafin ya bace wurin ya turnuke da bakin hayaki.
Bayanai sun ce wannan shi ne hatsarin farko na jirgin Boeing 787 Dreamliner wanda ya fara aiki a shekarar 2011.
Kamfanin Boeing ya ce tuni ya fara tattara bayanai don sanin hakikanin abinda ya faru.