Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya Ya Tabbatar Da Wajabcin Samun ‘Yancin Kan Falasdinawa

Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya ya fitar da wani kuduri da ya jaddada hakkin Falasdinawa tantance makomarsu da samun ‘yancin kai, da kuma wajabcin ‘yantar

Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya ya fitar da wani kuduri da ya jaddada hakkin Falasdinawa tantance makomarsu da samun ‘yancin kai, da kuma wajabcin ‘yantar da su daga duk wani kangin mamaya

Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya ya dogara da bayanan kwamitinsa mai kula da kare hakkin bil adama da jin kai, don haka ya zartas da wani kuduri da ke tabbatar da hakkin al’ummar Falasdinu na cin gashin kansu ta tantance makomar kasarsu da kansu da kuma hakkinsu na samun cikakken ‘yancin kai da kuma kubuta daga mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila ba tare da bata lokaci ba, saboda hakki ne wanda ba za a iya rabawa ba, kuma ba zai kasance a ƙarƙashin kowane sharuɗɗa ba, kuma ba za a iya sasantawa a kai ba, ko fakewa da matakan tsaro ba da gwamnatin mamayar Isra’ila ta ƙirƙira.

Matakin ya kuma jaddada abin da kotun kasa da kasa ta bayyana a cikin ra’ayoyinta na ba da shawara dangane da rashin halaccin haramtacciyar kasar Isra’ila na yin babakere kan harkokin Falasdinawa don haka babban zaunan Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci kawo karshen duk wani tsoma bakin yahudawan sahayoniyya a harkokin Falasdinawa cikin gaggawa, tare da hanzarta bai wa al’ummar Falasdinu damar yin amfani da ‘yancinsu na cin gashin kai da wanzar da makomar kasarsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments