Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa karfin bangaren sojojin tabbatar da zaman lafiya na majalisar a duniya, yana dai dai da karfin dukkan kasashen da suke bawa kudaden da ake tafiyar da ayyukansu ne. Don haka ya bukaci kasashen da basu biya rabonsu na kudade karo-karon da ake yi don tafiyar da ayyulan zaman lafiya a duniya bas u yi hakan da gaggawa.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto babban sakataren yana fadar haka a jiya talata ya kuma kara da cewa a halin yanzu majalisar tana tafiyar da ayyukan zaman lafiya har 11 a kasashen duniya wadanda suka hana da nahiyar Afirka Asia da kuma turai. Guterres ya kara da cewa majalisar tana da sojojin tabbatar da zaman lafiya a kasashen Congo, Afirka ta tsakiya, Sudan ta Kudu, Lebanon, Cyprus da kuma Kosovo.
Ya ce abinda ake bukata don tafiyar da 9 daga cikin ayyukan tabbatar da zaman lafiya 11 da Majalisar take da su, ya kai dalar Amurka billiyon $5.6 wanda yayi kasa da kasha 8.2% na abinda ta kashe a shekarar da ta gabata.
Labarin ya kara da cewa dukkan kasashen duniya 193, mambobi a MDD suna da abinda aka ware mata na kudaden da zata gabatar saboda tabbatar da zaman lafiya a duniya. Guterres ya kammala da cewa MDD ce take gaba a ayyukan tabbatar da zaman lafiya a duniya.