Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah wadai da kisan gillar da haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi wa Falasdinawa a Beit Lahiya
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres yayi Allah wadai da harin wuce gona da iri da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan garin Beit Lahiya da ke arewacin Zirin Gaza, wanda ya kai ga wani mummunan kisan kiyashi inda suka kashe dimbin Falasdinawa fararen hula da suka hada da yara da mata.
Wannan ya zo ne a cikin wata sanarwa da kakakin Majalisar Dinkin Duniya Stephane Dujarric ya fitar a jiya Laraba, dangane da matsayin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya kan kisan kiyashin da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi a Beit Lahia a ranar Talata.
Sanarwar ta yi nuni da cewa, Guterres ya yi matukar kaduwa da labarin kashe mutane da dama da suka hada da kananan yara, sakamakon harin da sojojijn haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai a Beit Lahia.
A cewar sanarwar, Guterres ya bayyana matukar yin Allah wadai da kisan gilla da raunata da kuma raba dimbin fararen hula muhallinsu