Babban Mufti na masarautar Oman ya yi kakkausar suka kan kasashen da ke neman kulla alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila
Babban Mufti na masarautar Oman, Sheikh Ahmed bin Hamad Al-Khalili, ya bayyana mamakinsa kan yadda wasu kasashe ke son kulla alaka da makiya yahudawan sahayoniyya, wata kasa ‘yar mamaya maras tushe.
A cikin wani bayani da ya wallafa a shafinsa na X, Ahmed bin Hamad Al-Khalili ya ce: “Abin mamaki ne yadda wasu kasashe ke son kyautata alaka da makiya yahudawan sahayoniyya, alhali su kansu suna kallon wannan mahalukiya a matsayin wata kasa mai gushewa ko ba dade ko ba jima, al’ummarta dai suna son ci gaba da yakin ne kawai don ci gaba da wanzuwarta, in ba haka ba, babu wanda a can yake son ci gaba da zama a wannan kasa bayan sun ga cewa hakan ba ya cikin maslahar rayuwa.”
Al-Khalili ya ce: “Ta yaya wadanda suke da tushe zasu kulla alaka da gwamnati da zata gushe da hukuma wacce zata gushe ko ba dade ko ba jima.?
Babban Mufti na masarautar Oman ya kara da cewa: “Idan kana son sanin girman bala’i da girman masifa, to ka yi tunanin yadda alakarka zata kasance da mai dabi’ar dabbobi mai kashe fararen hula daga yara da mata da kuma tsofaffi, ta yaya zai kare maka naka hakkokin? Ya karkare bayanin da cewa: “Mutum ya halaka a cikin kwanakinsa na jarrabawa…idan baya iya bambance tsakanin mai kyau da maras kyau.