Shugaban kasar Sudan kuma babban kwamandan sojojin kasar Janar Abdulfattah Alburhan, ya yi watsi da shawarar Amurka ta kawo karshen yaki a kasarsa wanda ya lakume rayukan mutane da dama, ya kuma raba kasar gida biyu a cikin watanni kimani 30 da suka gabata.
Shafin yanar gizo na labarai ‘AfricaNews’ ya nakalto Burhan yana fadar haka a ranar Lahadin da ta gabata jim kadan bayan ganawarsa da tawagar kasar Amurka wacce ta gabatar masa da shawarar, ya kuma bayyana ta a matsayin mafi munin shawarar tsagaita budewa juna wuta da aka gabatar masa ya zuwa yanzun.
Burhan ya zargi Massad Boulos mai bawa shugaban kasar Amurka shawara a kan al-amuran nahiyar Afirka da da kokarin rusa sojojin kasar Sudan da kuma bawa yan tawaye karkashin jagorancin Amity damar ci gaba da iko da wani bangaren kasar Sudan.
Burhan ya zargi Amurka da goyon bayan yan tawayen a cikin shawarar da ta gabatar, kuma shawarar ba irin zaman lafiyan da mutanen sudan suke so ba.
Masanadai suna ganin gwamnatin Amurka da kawayenta wadanda suke goyon bayan yantawayen a duniya musamman a cikin kasashen Larabawa, suna son sake raba kasar Sudan ne, kuma sun gabatar da wannan shawarar ce a dai-dai lokacinda suka fahinci cewa gwamnatin kasar tana samun nasara a kan yan tawaye wadanda suke iko da yankin Darfur na yammacin kasar ta Sudan.