Kungiyar gwagwarmayar Musulunci a kasar Lebanon – Hezbollah ta bayyana cewa, abin da ya faru yau wani babban kwanton bauna ne a kusa da kan iyakar Lebanon da Falasdinu.
Abubuwan da ke faruwa ba a saninsu saboda karancin bayanan da gwamnatin Isra’ila ta ba da umarnin kada a buga, duk da haka, bayanan da Sashen Kafafen Yada Labarai na gwagwarmaya na Sojoji suka fitar sun nuna cewa mayaka sun yi ta arangama da sojojin Isra’ila cikin dare.
Da karfe 11:00 na dare (lokacin cikin gida) a ranar Juma’a, mayakan Hezbollah sun sanya ido kan sojojin kasa na Isra’ila, wadanda ke yunkurin kutsawa cikin garin Odeissah da ke kan iyaka.
An yi wa rundunar kwanton bauna ne daga bisani kuma an yi artabu da makamai a yankin, wanda aka yi ta gwabza kazamin fada a ‘yan kwanakin da suka gabata.
Yankin Odeissah ya kuma shaida kisan akalla hafsoshi da sojojin Isra’ila tara daga sashin Egoz na runduna ta 98 da kuma na Yahalom a ranar Alhamis.