Araqchi : Zan Samar Da Hanyoyin Tunkarar Takunkuman Da Aka Kakabawa Iran

A rana ta biyu na muhawara a majalisar dokokin Iran kan jerin sunayen ministocin da shugaban Kasar Massoud Pezeshkian ya gabatar, Abass Araqchi wanda aka

A rana ta biyu na muhawara a majalisar dokokin Iran kan jerin sunayen ministocin da shugaban Kasar Massoud Pezeshkian ya gabatar, Abass Araqchi wanda aka gabatar a mukamin ministan harkokin wajen kasar a sabuwar gwamnatin, ya kare manyan abubuwan da ya sa a gaba, ciki har da hanyoyin tinkarar takunkumin da aka kakabawa kasar ta Iran.

Ya ce za a gudanar da shirye-shiryen cire takunkumin ne tare da hadin gwiwa da ‘yan majalisar dokokin Iran, inda ya kara da cewa za a yanke duk wata matsaya ta hanyar fahimtar juna.

Ya kuma jaddada cewa Iran ba za ta amince da yin gaggawar tattaunawa ba game da dage takunkumin.

Sabin manufofin harkokin waje na gwamnatin Iran za su dogara ne kan hanyoyin karfafa tattalin arziki da martabar kasar, in ji Araqchi, tsohon mai shiga tsakani kan batun nukiliyar kasar.

Iran ta soki rashin kyakyawar anniyar Amurka da kasashen turai na E3 wajen farfado da yarjejeniyar, wanda ya sanya Iran daukar matakin indagnta ayyukanta na nukiliya a matsayin maida martini.

Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya nada a matsayin ministan harkokin wajen kasar Abbas Araqchi, wanda shi ne tsohon mai shiga tsakani kan batun nukiliyar kasar, kuma ya ce zai dukufa akan neman hanyoyin dage wa kasar takunkumi  idan har majalisar dokokin kasar ta amince da nadin nasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments