Araqchi: Hamas na raye, za ta ci gaba da kara karfi fiye da kowane lokaci a baya

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas tana nan a raye kuma za ta ci gaba da tafiya a

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas tana nan a raye kuma za ta ci gaba da tafiya a kan turbar da take duk da shahadar shugabanta Yahya Sinwar.

Araghchi, wanda ya kai ziyarar aiki a Turkiyya a matsayin shugaban tawagar diflomasiyya don halartar dandalin hadin gwiwar yankin kudancin Caucasus na 3+3 a Istanbul, ya gana da manyan jami’an Hamas a wannan Asabar.

“Abu daya da yake da muhimmanci kowa ya sani shi ne, bayan shahadar Sinwar da sauran manyan jagorori  a Gaza, Hamas na nan a raye kuma za ta ci gaba da tafiya a kan turbarta ta gwagwarmayar neman ‘yanci, Kamar  Araghchi ya fadawa manema labarai bayan taron.

Ya ci gaba da cewa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta gaza cimma ko daya daga cikin manufofinta bayan shafe shekara guda tana yakin kisan kare dangi a Gaza, duk da cewa ta yi dukkan kokarinta tare da kashe sama da mutane 50,000 tare da lalata gidaje da dama, tare da aikata laifuka da dama da kowa ya sani.

Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya kara da cewa, ya yi cikakkiyar tattaunawa da mambobin ofishin siyasa na kungiyar Hamas kan yakin zirin Gaza, da shawarwarin tsagaita bude wuta da ma sauran batutuwa.

A yayin ganawarsa da Mohamed Ismail Darwish shugaban majalisar shura ta Hamas, Araghchi ya jaddada cewa yawan cin zarafi da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta yi a Gaza a cikin shekarar da ta gabata ya haifar da dawwamammen abin kunya ga gwamnatin yahudawan da masu magoya bayanta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments