Ministan Harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Dole ne ƙasashen yankin su tabbatar da tsaron kansu, kuma Iran a shirye take ta taimaka
Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa: “Dole ne kasashen yankin su tabbatar da tsaron kansu, kuma Iran a shirye take ta taimaka wajen cimma wannan muhimmin aiki, amma babu wata hanya da fi hakan.”
A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Mehr, yayin bikin kaddamar da “Cibiyar Adana Muhimman Takardu da Gidan Tarihi na Shahidi Sayyid Kamal Kharrazi” a ranar Lahadin nan, Araqchi ya bayyana cewa: Wadannan kalaman sun sake jaddada hangen nesa da marigayi Dr. Kharrazi ya gabatar kimanin shekara daya da rabi da suka wuce—a yayin taron “Tattaunawa tsakanin Iran da Larabawa”—dangane da manufofin yankin.
Ya jaddada daidaiton tsarin Iran duk da barkewar manyan yaƙe-yaƙe guda biyu a yankin, yana mai jaddada kudirin kasarsa na cimma zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin ta hanyar dogaro da kai ga kasashen da abin ya shafa, ba tare da tsoma baki daga kasashen waje ba.
A cikin nazarinsa kan yaƙe-yaƙen yankin, Ministan Harkokin Wajen Iran ya yi la’akari da yaƙe-yaƙen da aka gani a yankin a lokacin da ya gabata a matsayin wani muhimmin abu da ya haifar da wargaza tsarin tsaro da ake da shi da kuma sauyin daidaiton yanki, yana mai tabbatar da cewa halin da ake ciki a yanzu ba zai koma yadda yake a baya ba.