Arakchi: Mun dakatar da musayar sakonni tsakaninmu da Amurka

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi, ya tabbatar da cewa an dakatar da duk wata tuntubar juna tsakanin Iran da Amurka ta hanyar masu

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi, ya tabbatar da cewa an dakatar da duk wata tuntubar juna tsakanin Iran da Amurka ta hanyar masu shiga tsakani, saboda yanayin da ake ciki a halin yanzu a gabas ta tsakiya.

Araqchi ya bayyana hakan ne a wannan Litinin a babban birnin kasar Omani, Muscat, inda ya ce, a ko da yaushe masarautar Oman tana taka rawar da ta dace dangane da tuntuba  tsakanin Tehran da Washington domin isar da sako ko samar da hanya ta  yin shawarwari.

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya sanar da cewa, kasarsa ta daina yin musanyar sakonni da Amurka a cikin yanayi na musamman na yankin, yana mai cewa “babu wani tushe da ya dace na aiwatar da musayar sakonni a halin yanzu.”

Araqchi ya ce a ziyarar da ya kai birnin Muscat, babban birnin kasar Oman, masarautar kasar  ta kasance mai matukar taimakawa wajen magance matsalolin da ke addabar yankin gabas ta tsakiya.

Ya kuma yi nuni da cewa, “Lokacin da aka shawo kan wannan rikici da ake  ciki, za mu yanke shawarar ko za mu koma kan hanyar musayar sakonni da Amurka da kuma yadda za a a aiwatar da hakan.

Ya yi jawabi ga Amurka da kasashen Turai, yana mai cewa: “Matsayin Iran a bayyane yake cewa ba ta son yaki, amma a shirye take ta tunkari kowace barazana ko tsokana,” ya ci gaba da cewa: “Mun yi imanin cewa tilas ne diflomasiyya ta yi tasiri da kuma hana barkewar babban rikici a yankin.”

Har ila yau Araqchi ya jaddada cewa, alakar da ke tsakanin Iran da masarautar Oman ta ginu ne kan abokantaka, mutunta juna, da hadin gwiwa kan batutuwa da dama da ke kara kusantar kasashen biyu ga manufofinsu

Tun da farko a yau Araqchi ya yi kira ga takwaransa na Oman Badr bin Hamad Al Busaidi, kan wajabcin yin aiki tare domin gaggauta dakatar da kisan kiyashi da wuce gona da iri da haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi kan zirin Gaza da Lebanon, yana mai kira da a kara kokarin kai agaji na kasa da kasa ga ‘yan gudun hijira.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments