Iran: Rashin Hukunta Amurka Zai Raunana Dokokin Kasa Da Kasa

Amurka da Isra'ila sun sake kai wani hari kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu.

Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya yi gargadin cewa rashin daukar matakin da ya dace kan Amurka da Isra’ila saboda hare-haren da suka kai kan Iran, zai raunana dokokin kasa da kasa tare da sanya tsaron kowace kasa cikin hadari.

A cikin wata makala da kamfanin dillancin labarai na Kyodo News ya wallafa, Araghchi ya sake jaddada cewa hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran “sun saba wa dokar da ta haramta amfani da karfin soja a fili, kuma sun take ‘yancin ikon mallakar kasa na Iran”.

Ya kara da cewa, “Harin sojan da Amurka ta kai kan Iran bai samu amincewar Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ba; haka kuma, zargin cewa za a iya samun barazana a nan gaba, shi kadai, bai isa ya zama hujjar doka ta kare kai ba.”

Ministan ya yi gargadin cewa illolin da ka iya tasowa sakamakon irin wannan take dokokin kasa da kasa, sun wuce “batun tsaron Iran ko daidaiton karfi a yankin Gabas ta Tsakiya kadai”.

Araghchi ya ce, “Abin da ke cikin hadari a karshe shi ne amincewa da tsarin dokokin kasa da kasa, wanda aka tsara domin hana kasashe amfani da karfin soja yadda suka ga dama.”

“Idan aka bar karfi ya yi rinjaye a kan doka, ba Iran kadai za ta sha wahala ba.

Tushen tsarin dokokin kasa da kasa, har ma da karfin doka na Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya, su ma za su shiga cikin hadari.”

Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya yi gargadin cewa, idan ba a hukunta kasashen da suka kai hari ba, to “ba za a iya daukar tsaron wata kasa a matsayin abin da ke da tabbas ba”.

Araghchi ya kuma jaddada cewa dole ne Amurka ta kawo karshen hare-haren da take kai wa Iran, ta mutunta ‘yancin mallakar kasa da iyakokin Iran, tare da biyan diyya kan barnar da hare-haren da ba su da tushe ko halaccin doka suka haifar.

Ya kuma jaddada cewa Iran “tana da hakkin kare kanta a karÆ™ashin Mataki na 51 na Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya don mayar da martani ga harin makami mai linzami”.

Amurka da Isra’ila sun sake kai wani hari kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu, kimanin watanni takwas bayan kai hare-hare ba tare da wani dalili ba a kan kasar.

Iran ta yi gaggawar mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka a yankunan da Isra’ila ta mamaye, da kuma sansanonin Amurka da muradunta a duk fadin yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted