Araghchi : Bai Kamata A Rika Murgude Hakkin Dan Adam Ana Shishigi A Harkokin Cikin Gidan Kasashe Ba

Ministan harkokin wajen kasar Iran, ya bayyana cewa bai kamata a yi amfani da hakkin dan adam a matsayin abun matsin lamba na siyasa ko

Ministan harkokin wajen kasar Iran, ya bayyana cewa bai kamata a yi amfani da hakkin dan adam a matsayin abun matsin lamba na siyasa ko tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kasashe ba.

Abbas Araghchi, ya bayyana hakan ne a zaman kwamitin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya, inda ya jaddada cewa, daya daga cikin manyan abubuwan da ke kawo cikas ga tabbatar da hakkin dan Adam a duniya shi ne amfani da matakan tilastawa kasashe.

Ya kara da cewa wadannan matakan suna da illa ga fararen hula kuma ba adalci ne ba ga marasa galihu kamar mata, yara, tsofaffi da masu nakasa.

Ministan harkokin wajen kasar Iran Seyyed Abbas Araghchi ya bayyana jin dadinsa a wannan zama inda Ya ce: Jamhuriyar Musulunci ta Iran a matsayinta na daya daga cikin kasashen da suka assasa Majalisar Dinkin Duniya, a ko da yaushe tana mutunta daidaito da adalci a matakin koli. »

Araghchi ya bayyana cewa shekaru da dama da suka gabata al’ummar Iran na fuskantar manyan kalubale kamar takunkumin karya tattalin arziki da kuma ta’addanci, wadanda suka yi illa ga hakkokinsu na zamantakewa da tattalin arziki, To sai dai kuma a cewarsa duk da wadannan kalubale, Iran ta samu ci gaba mai ma’ana A tsarin Musulunci da mutuncin bil’adama, da inganta fannonin ilimi da kiwon lafiya da ‘yancin mata da ci gaban masana’antu da tattalin arziki.

Muna bukatar a gaggauta soke duk wani takunkumi, saboda ba wai kawai take hakkin bil’adama na al’ummar Iran ba ne, har ma da haifar da wahala ga miliyoyin mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments