Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa masu aikiwa HKI a Amurka da sauran kasashen yamma suna kokarin sako kirkiro wata karya Iran wacce suka bawa kansu damar fadawa kasar Iraki da yaki a shekara ta 2003, don a wannan karon su sake fadawa kasar Iran da sunan ta mallaki makaman kare dangi.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Aragchi yana fadar haka a shafinsa na X ya kuma kara da cewa, HKI tana ta amfani da kafafen yada labarai na kasashen yamma da kawayensu da kasashen yankin don yada karya kan cewa Jumhuriyar Musulunci ta IOran ta mallaki makaman kare dangi, don haka akwai bukatar a sake yin gangami don lalata wadannan makaman. Kamar dai yanda suka yi a shekara ta 2003 wanda ya basu damar mamayar kasar Iraki har na kimani shekaru 20 ba tare da sun sami makaman da suke zargin kasar Iraki ta mallaka ba.
A cikin sa’o’ii 72 da suka gabata, kafafen yada labarai na HKI da kawayentasun yada labaran karya kan cewa Tehran tana son ta yi amfani da makaman guba, kan Washington, sannan tana gina sansanin makamai masu linzami a karkashin madatsar ruwa ta RUBISH .
Wannan yana cewa ne bayan da CNN ta bada rahoton cewa, akwai yiyuwar Iran ta yi amfani da abinda suka kira makamai marasa tsabta a birnin Washington DC.
Sannan Jaridar the York Times ta bayyana cewa madatsun ruwa na jumhuriyar Musullunci ta Iran suna da nasaba da ayyukanta na gina makamai masu linzami.
Jumhuriyar Musulunci ta Iran dai ta musanta labarin ta kuma bayyana cewa manufar wannan farfagandar ita ce, sake shirin farwa kasar da wani yaki tare da taimakon kasashen yamma da kawayensu a duniya. Daga karshe ministan ya kammala da cewa, wannan shirimmu kamar wadanda suka gabata ba zai je ko ina ba. Kuma JMI a shirye take ta fuskanci ko wace Iran barazanar da suke mata.