Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa HKI tana kokarin fadada yakin da take fafatawa da Falasdinawa a Gaza zuwa sauran kasashen kudancin asiya.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Aragchi yana fadar haka a birnin New York na kasar Amurka inda ya isa a jiya Jumma’a don shirin halattar babban taron MDD karo na 79. Arachi ya na birnin New York don shirin zuwan shugaban kasa Masoud Pezeskiyan taron babban zauren MDD a cikin yan kwanaki masu zuwa.
Ministan ya kara da cewa hare haren HKI ta kasar Lebanon a cikin yan kwanakin da suka gabata, wadanda suka hada da na’urorin sadarwa na ‘Pager’ da kuma waki toky da kuma wadanda ta kai dahiya Junubiyya a birnin Beirtut sun nuna cewa tana son fadada wannan yakin a kasashen yankin ne. Ministan harkokin wajen kasar Iran ya kara da cewa a bisa laifuffukan da HKI ta yiwa JMI zata rama amma ba ta yadda hakan zai fadada yakin kamar yadda HKI take so ba.
Dangane da kissan Shahid Isma’ila Haniyya shugaban kungiyar Hamas a Tehran kuma, ministan yace dole ne Iran zata dauki fansar jininsa a wuri da lokacinda suka dace.
Aragchi yayi allawadai da kissan kwamandojin kungiyar Hizbulla daga ciki har da Ibrahim Aqil wanda yake cikin mutane 14 da suka yi shahada a harin jiya jumma’a. Gwamnatin kasar Lebanon ta tabbatar da cewa mutane 42 suka yi shahada sanadiyyar hare-hare na na’urorin sadarwan da HKI ta kai kan mutanen kasar, sannan wasu kimani 3’500 suka ji raini.