Ana Shirye-Shirye Fara Taron Koli Na Kasashen BRICS a Kasar Rasha

Rasha ta sanar da cewa shugabannin kasashe sama da ashirin za su hadu a Kazan na kasar a mako mai zuwa don taron koli na

Rasha ta sanar da cewa shugabannin kasashe sama da ashirin za su hadu a Kazan na kasar a mako mai zuwa don taron koli na kungiyar BRICS, wadda ƙawance ne na kasashe masu tasowa wadda Rasha ke fatan za su ƙalubalanci “danniyar” ƙasashen Yamma.

Sakataren MDD Antonio Guterres, da Shugaban China Xi Jinping, da shugaban Brazil Luis Inacio Lula da Silva, da shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan suna za su halarci taron a birnin Kazan, daga 22 ga Oktoba zuwa 24.

Rasha ta ce tana sa ran zuwan firaministan India Narendra Modi shi ma.

Moscow ta bayyana kokarin fadada BRICS, wanda saunan ya samo asali daga harafin farko na sunayen ƙasashen Brazil, Russia, India, China da Afirka ta Kudu, a matsayin wani ginshiƙin harkokin wajenta.

Babbar ajandar taron ƙoli na ƙungiyar BRICS ya hada da tsarin hada-hadar kudade tsakanin kasashen duniya wanda zai yi gogayya da tsarin SWIFT, sai kuma batun rikicin Gabas ta Tsakiya.

Kremlin ta kira taron a matsayin nasara diflomasiyya wadda za ta taimaka mata wajen gina kawance da zai kalubalanci “danniyar” Yamma.

Amurka ta yi watsi da batun cewa BRICS za ta zama “abokiyar adawa ta yanki” amma ta bayyana damuwa game da irin tasirin da Moscow take da shi mai karfi a cikin lamarin kungiyar, wanda ba zai tafi bisa mahanga guda da irin mahangar tsarin jari hujja na Amurka ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments