An Zargi Sojojin Mamayar Isra’ila Da Kokarin Shafe Al’ummar Tel-Al-Hawa Daga Kan Doron Kasa

Kungiyar Hamas ta bayyana cewa: Muggan laifukan da sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suka aikata a Tel al-Hawa kokarin shafe al’umma ce daga kan doron

Kungiyar Hamas ta bayyana cewa: Muggan laifukan da sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suka aikata a Tel al-Hawa kokarin shafe al’umma ce daga kan doron kasa

Kungiyar Hamas ta bukaci kasashen duniya da su dauki matakin gaggawa kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila dangane da muggan laifukan da ta aikata a yankin Tel al-Hawa da ke kudu maso yammacin birnin Gaza.

A cikin wata sanarwa da kungiyar ta Hamas ta fitar a jiya Juma’a ta bayyana cewa: Ayyukan ta’addancin da sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suka aiwatar a shiyar Tel al-Hawa, bayan shafe kwanaki suna sintiri a cikinta tare da kaddamar da munanan hare-haren bama-bamai kan dukkanin bangarorin rayuwa, hakan laifukan yaki ne kuma kisan kare dangi, da kokarin shafe wata al’umma daga kan doron kasa.

Hamas ta Ta kara da cewa: Sojojin mamayar sun kona wasu gine-gine kafin su bar shiyar ta Tel al-Hawa, tare da hana jami’an tsaron farin kaya isa ga gine-ginen da suka kone tare da dukkan iyalansu da suke ciki, inda wasu rahotonni suke tabbatar da cewa gawarwakin iyalan da suka yi shahada suna warwatse a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments