Dubban masu zanga-zanga ne suka fito kan titunan kasar Jordan da kasar Iraki domin yin Allah wadai da shirin shugaban Amurka Donald Trump na korar Falasdinawa daga yankin Gaza.
Masu zanga-zanga a Amman babban birnin kasar Jordan, da kuma wasu garuruwan kasar Larabawa, sun yi zanga-zangar nuna adawa da shirin na tilastawa mazauna zirin Gaza kaura.
A Jodan an gabatar da wani sabon daftarin doka a majalisar dokokin kasar da zai haramta tilastawa Falasdinawa komawa Jordan.
An kuma gudanar da zanga-zangar adawa da shirin a Bagadaza babban birnin kasar Iraki, baya ga Masar inda aka yi irin wannan zanga-zangar.
Yayin ganawarsa da firayi ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a ranar Alhamis, Trump ya bayyana shirinsa na kwace yankin Gaza na Falasdinu tare da korarsu daga yankin inda ya bukaci kasashen Masar da Jordan dasu karbe su duk da cewa kasashen biyu sun yi watsi da shirin a hukumance.
Shirin na Trump, ya ci karo da tofin Allah tsine daga shugabannin kasashen duniya da dama da kuma babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya.